Thursday, 15 August 2019

Adam A. Zango ya ce ya fita daga Kannywood

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, ya ce ya fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.


Jarumin ya ce daga yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sai dai bai yi karin haske ba sosai game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar ba, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood.

Kodayake Zango ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda zargin yadda ake shugabancin kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki "saboda kwadayi da son zuciya."

Daga nan ya ce shi ya koma "mai shirya fina-finai mai cin gashin kansa."

A karshe ya ce yana maraba da duk wanda zai yi aiki da shi, "amma ban da Kano don kada na karya dokar 'yan Kannywood," a cewarsa.

BBC ta yi kokarin tuntubar dan wasan domin neman karin bayani kan lamarin amma bai amsa wayarmu ba kawo yanzu.

Hakazalika shi ma jarumin fina-finan Hausa Misbahu M Ahmad ya wallafa wani bidiyo inda yake bayyana bacin ransa ga Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu a shafinsa na Instagram.

Misbahu ya zargi shugaban hukumar da hannu a kama wani abokin aikinsu wato wani Sanusi Oscar.

Amma shugaban hukumar ya bayyana cewa an kama Oscar ne saboda ya saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata wakarsa wadda akwai "badala a ciki," a cewarsa.

Afakallahu ya bayyana cewa sun jima suna bibiyar Oscar domin su kama shi, amma sai a 'yan kwanakin nan ne suka samu damar yin hakan.

Daga nan ya sha alwashin cewa ba za su ji tsoron maganganun da wasu suke yi cewa siyasa ce ta sa aka kama Sanusi, inda ya sha alwashin za su ci gaba da yin aikinsu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment