Saturday, 10 August 2019

Aikin hajji: Miliyoyin Musulmai na addu'o'i a dutsen Arfa


Mahajjata sun taru a Arfa a matsayin aiki mafi muhiimnaci na aikin hajji
Aikin hajji da musulmai kan yi a kowace shekara ya kai matuka a yau, inda mutane kimanin miliyan biyu da rabi suka taru a dutsen Arfa inda za su wuni suna addu'o'i tare da karatun alkur'ani.


Mahajjatan sun taru a kan wannan dutse da filin da ke makwaftaka da shi ne a gab da fitowar rana.
Wannan wuri na Arfa na da nisan kimanin kilomita 15 daga birnin Makka.
A wannan dutse ne dai annabi Muhammad (S.A.W) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, wadda ake kira hudubar ban-kwana.
Aikin Hajji na daga cikin ginshikan Muslunci guda biyar, wanda ake so musulmi ya aikata akalla sau daya a tsawon rayuwarsa.
Mahajjata dai na fitowa ne daga dukakkanin fadin duniya, to amma Indonesia wadda ita ce ta fi kowace kasa yawan Musulmai a duniya, ita ce ta fi kowace yawan Musulmai a wurin na aikin hajji.
Daya daga cikin darussan da aikin hajji ke koyarwa shi ne karfafa dangantaka, da kuma nuna cewa kowane dan'adam daidai yake a gaban Allah madaukaki.
A lokacin aikin dukkanin mahajjata kan sanya sutura iri wadda ake kira ihrami.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment