Wednesday, 21 August 2019

Akarshe dai Kwamfuta ta raba gadda kan wanda yafi iya kwallo tsakanin Ronaldo da Messi

A bunda ya dade ana tattaunawa tsakanin masoyan kwallon kafa shine wa ye babban gwani ko kuma wa ya fi wani tsakanin taurarin kwallon biyu a wannan zamani watau Cristiano Robaldo da Lionel Messi.Wannan yasa wasu farfesoshi daga jami'ar KU Leuven ta kasar Belgium suka hadu dan raba gardama tsakanin masoya kwallon kafar inda suka yi amfani da na'ura me kwakwalwa ta musamman.

Masu bunciken sunce sun yi amfani da bayanai da suka samu daga kasar Netherlands inda aka tattara bayanai daga kakar wasannin shekarun 2013/14 zuwa 2017/18 da Ronaldo ya bugawa Real Madrid wasa, sannan an yi amfani da cin kwallaye da taimakawa wajan cin kwallaye da kuma yin wasa da kwallo wajan yanke wannan hukunci.

Bayan tattara bayanan an zubawa kwamfuta ta musamman dan ta raba gardama inda kuma kwamfutar ta zabi Messi a mtsayin wanda yafi zama gwani akan Ronaldo.

Saidai ba lallaine musamman masoya Ronaldo su yadda da wannan hukunci ba inda wasu ke cewa ma ai basu yadda da fasahar kwamfutar ba dan kuwa itama ai zata iya yin kuskure.

Wasu kam na cewa Eh! Messi Gwanine wajan sarrafawa da cin kwallo kamar Aljani wanda shi iya kwallonshi kamar haihuwarshi aka yi da ita amma abinda ke burgesu da Ronaldo shine shi da kanshine ya jajirce ya koya yake kuma kokarin yin kankan da Messin.


Koma dai menene duka wadannan 'yan kwallo gwanayene da Duniya ba zata taba mantawa dasu ba indan aka zo tarihin bajinta a kwallon Duniya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment