Thursday, 8 August 2019

Alex Iwobi ya bar Arsenal zuwa Everton

Rahotanni daga Ingila na cewa a yayin da aka kulle kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa, tauraron dan kwallon Arsenal, Alex Iwobi ya koma kungiyar kwallon Everton akan fan miliyan 38.
Rahoton ya ci gaba da cewa Iwobi zai sakawa Everton hannu akan buga mata wasa na tsawon shekaru 5.

Arsenal ta kuma sayo dan wasan Celtic, Kieran Tierney akan fan miliyan 25.

Hakanan a yau din dai Dan wasan Chelsea, Danny Drinkwater ya bar kungiyar zuwa Burnley akan aro har zuwa watan Janaru.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment