Thursday, 8 August 2019

Alhazai miliyan 1.8 ne za su yi hajjin bana>>kasar Saudiyya


Darakta Janar na hukumar kula da bayar da fasfon kasar Saudiyya, Majo Janar Sulaiman Bin Abdulaziz Al-Yahaya ya bayyana cewa mutane miliyan 1.8 ne suka isa kasar Saudiyya dan gudanar da aikin hajjin bana.

Da yake jawabi ga 'yan jarida jiya, Laraba a Jidda, Al-Yahaya yace mutane miliyan 1, 708,152 ne suka isa Saudiyya ta jiragen sama sannan guda 94, 388 kuma suka isa kasar ta bodojin kasa, sai kuma guda 17, 250 da suka isa kasar ta jiragen ruwa, ya kuma bayyana cewa, an samu Visar bogi guda 300 yayin da ake tattara bayanai.

Al Yahaya ya bayyana cewa tuni har sun fara ayyukan mataki na gaba watau mayar da mahajjata kasashensu bayan sun kammala aikin hajji sannan ya gargadi cewa duk mahajjacin da aka kama ya tsaya a kasar bayan kammala aikin hajji zai fuskanci fushin hukuma.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment