Thursday, 22 August 2019

An gano yarinyarnan data bace Gidan wani mutum a Abuja

Yarinyarnan 'yar Jos me suna Halima da labarinta ya karade shafukan sada zumunta cewa daga zuwa ta hadu da wani da suka hadu ta shafin sada zumunta ta bace ba'a kara jin duriyarta ba a karshe dai an gano ta a gidan wani mutum a babban birnin tarayya, Abuja.Wata 'yar uwarta Halima da tun a farko ta wallafa labarin bacewar 'yar uwartata a shafinta na Facebook ce ta sake fitowa a wannan karin kuma ta bayyana cewa an ga A'adiya a gifan wani mutum data wallafa hotunanshi a shafinta na Facebook da tace a Abuja yake.

Ta kara da cewa ba Sa'adiya bace kadai a gidan mutumin ba an samu kuma waau sauran 'yan mata.

Ga dai abinda ta rubuta kamar haka:

"Allahamdulillahi

 Ansamu Labarin Mutunmin Da Yazo Ya Dauki Cousin Sister Dinmu, Kuma ba Ita Kadai Bane A Gidan Da Ya Kaita Akwai Yammata Da Yawa Wanda Aka Sake Suna Gidan A Abuja.
Allah Ya Kara Tona Asirin Su!! Mun Gode Da Adu'an Ku🙏🙏🙏.
More Details Later Inshaa Allah"


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment