Monday, 5 August 2019

An gindaya wa Zakzaky sharuddan fita Indiya

Damar da babbar kotun a Kaduna ta bai wa Sheikh Ibrahim Zakzaky ta fita kasar waje tana tattare da wasu sharudda da kotun ta ce lallai sai an cika su.


A safiyar ranar Litinin ne dai kotun ta ba shi damar zuwa kasar Indiya domin neman magani, kamar yadda lauyoyinsa suka nema.
Lauyoyinsa sun bayyana cewa shugaban kungiyar ta IMN yana fama ne da matsalar ido, inda suka ce "ya fara daina gani baki daya yayin da ake yi masa shari'a."
Sannan lauyoyin sun ce har yanzu akwai matsalar harsashin bindiga a jikinsa, sanadiyyar harbinsa da aka yi kansa, a cewarsu.
Yayin zaman kotun, alkalin kotun ya shardanta cewa lallai ne jami'an gwamnati su yi wa Zakzaky rakiya zuwa kasar ta Indiya.Lauyan da yake kare Zakzaky Sadau Garba ya shaida wa BBC cewa lauyoyin gwamnati sun bayyana fargabar cewa idan Zakzaky ya fita daga Najeriya, "ba lallai ne ya dawo ba."
"Wannan shi ne dalilin da ya sa kotun ta saka sharadin cewa jami'an gwamnati ne za su yi masaa rakiya," in ji shi.
Lauyan gwamnatin Najeriya a shari'ar Bayero Dare ya shaida wa BBC cewa kotun ta ba shi damar fita ne kawai domin neman lafiya "saboda da mai rai kadai ake yin shari'a".
"Kotu ta ba shi damar fita kamar yadda lauyoyinsa suka bukata domin ya nemi magani. Mun bayyana fargabarmu ga kotun amma sai ta ce ai da mai rai ake shari'a ba matacce ba," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Abin da hukuncin ke nufi shi ne za a saki Zakzaky ba tare da bata lokaci ba, bayan an gama shiryen-shiryen tafiyar."
BBCHausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment