Sunday, 11 August 2019

An Shiga Har Cikin Gidansa Aka Yi Masa Yankan Rago A Kano

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!

A daran jiya Arfat ne ranar mai daraja aka samu wasu mara imanin da ba a san ko su wanene ba suka haura har cikin gidan Mallam Muhammad wanda aka fi sani da Baffayo suka yi masa yankan Rago a Dorayi Babba Unguwar Jakada haifaffan Unguwar Sani Mainagge duk a yankin karamar hukumar Gwale jihar Kano, kuma a lokacin da lamarin ya faru mai dakin Marigayin bata nan sai shi kadai a gidan.


Kuma bayan faruwar lamarin Marigayi Baffayo saboda karfin hali da kan sa ya sakko daga kan benen gidan sa bayan sun yi masa wannan cin amanar, Ya fito inda ya dafe wuyan sa da ka yanka jini na diban sa haka har Allah ya ba shi ikon fitowa neman taimakon makoftan sa kafin ka ce me aka garzaya Asibiti da shi kafin ka ce me rai ya yi halin sa.

Kafin rasuwar Baffayo dan kasuwa ne da yake yin safarar Dabino Tirela Tirela daga Janhuriyar Nijar zuwa sassan yankin arewacin Najeriya, rasuwar sa ta kidima 'yan uwa da abokan sa inda suke cewar tabbas an yi rashin mutumin kirki wanda yake zaune lafiya da al'umma musamman a Unguwar su ta Sani Mainagge, inda ya zuwa yanzu hukumar 'yan sanda suka dukufa domin gano miyagun da suka aikata wannan mummumar ta'asar.

Allah ya ji kan sa ya karbi shahadarsa. Ya Allah ka kawo mana dauki, ka yi mana maganin wannan bala'in daya tunkaro mu a wannan jihar da kasar ga baki daya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment