Sunday, 25 August 2019

APC da PDP sun biyani miliyan 19 dan in musu aiki su ci zabe>> Gogarman me garkuwa da Mutane da yayi sanadiyyar kisan 'yansanda

A ci gaba da bayanan dake fitowa bayan kama rikakken kuma attajirin me garkuwa da mutane, Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume, da yayi sanadiyyar kisan 'yansanda ya bayyanawa manema labarai cewa shi ba me garkuwa da mutane bane amma shi dan bangar siyasane kuma yana yaudarar 'yan siyasar da cewa yana da sihirin da zai musu su ci zabe sannan yana sayarwa da masu garkuwa da mutane makamai.A hirar da Jaridar Vanguard ta yi da Wadume ya bayyana yanda ya ajiye harkar karatu a gefe tun yana karamar sakandire ya kama sana'ar kifi.

Wadume yace daga baya ya shiga harkar bangar siyasa inda ya rika samun makudan kudade, yace wani gwamna me ci ya bashi kudi miliyan 6 dan ya mai aiki ya kuma sa wasu malamai su mai aiki dan ya ci zabe.

Yace, sun hadu da gwamnanne a yayin da yazo garinsu na Ibi yakin neman zabe, shi kuma Wadume shine shugaban matasan yankin, sun kebe suka gana, a nanne yawa gwamnan Alkawarin yimai addu'a dan ya ci zabe, ya bashi miliyan 2 dan a fara aiki.

Yace daga baya ya kirashi ya kara mai miliyan 4 dan a ci gaba da addu'a. Bayan yaci zabe, ya kira Wadume ya mai godiya.

Yace a zaben shugaban kasa ma jam'iyyar APC ta bashi miliyan 13 dan ya mata aiki taci zabe, amma miliyan 7 kawai ya kashe a cewarshi, ya kara da cewa ya kuma damfari wani ma'aikacin gwamnati miliyan 30.

Wadume ya kara da cewa ya kuma taba neman kujerar dan majalisar jiha amma ya janye.

Yace ranar da 'yan sanda suka zo kamashi yana shan shayine da abokanshi inda suka nunamai shedar aikinsu sukace an turosune su kamashi. Ya kara da cewa be musu gaddama ba kasancewar yasan duk runtsin da ya shiga zai iya fitar da kanshi.

Yace shi be gayawa Captin din sojan da ya kubutar dashi daga hannun 'yan sandan cewa an kamashi ba kuma be san ma wanda ya gayamai cewa an kamashiba.

Ya kara da cewa 'yansandan sun saka mai ankwa a kafa da hannu, sun wuce shingen tsaro na daya dana biyu,a na 3 ne 'yansandan da suka kamashi sun sauka dan nunawa abokan aikinsu shedar aiki sai kawai sojoji suka zo suka bude musu wuta.

Nan shima ya samu rauni kamar yanda yace, suka tafi dashi gidan Kaftin Balarabe, anan hadda gawarwakin 'yansandan,ina ganin gawarwakin 'yansandan sai naji banji dadi ba, yace a nanne ya sulale ya tsere daga hannun sojojin.

Wadume ya kara da cewa a lokacin akwai dubu 500 a jikinshi, sai ya nemi wani yaronshi suka tafi gidanshi, acan ma sai sojojin suka biyoshi, yace da ya gansu kuma yaga alamar kasheshi zasu yi, sai ya sake tserewa ya tafi Kano gidan wani dan uwanshi.

Wadume ya kara da cewa da yana Kano ya kira wani dan uwanshi yace ya je gidanshi ya dauke bindigogin dake gidan ya boye mai su.

Sannan kuma ya bayar da miliyan 3 dan a baiwa 'yan jarida su rubuta labari me kyau akanshi saboda sunanshi na neman baci.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment