Friday, 9 August 2019

Arsenal ta kammala sayen David Luiz daga Chelsea

Kungiyar Arsenal ta kammala sayen dan wasan baya na Brazil David Luiz daga Chelsea a kan kudi fan miliyan 8, a kwantiragin shekara biyu.


Luiz, mai shekara 32, wanda kwantiraginsa zai kare a shekarar 2021, da Chelsea bai yi atisayi da tawagar manyan 'yan kwallon kungiyar ba a ranar Laraba.

Sai dai dan wasan mai shekara 32 ya halarci atisayen a Cobham kuma bai bijire wa wani umarni ba - amma dai ba a yi komai da shi ba.

Bayan da Chelsea ta sayo dan wasan daga Benfica a watan Janairu na 2011, a kan fam miliyan 21, Luiz ya tafi PSG a watan Yuni na 2014 inda kungiyar ta Faransa ta saye shi a lokacin a kan fan miliyan 40, kafin kuma daga baya ya koma Stamford Bridge din a Agustan 2016 a kan fan miliyan 34.

Gaba daya ya yi shekara shida da rabi a Chelsea, inda ya dauki kofin Premier, da na FA biyu, da na Zakarun Turai na Champions da kuma na Europa biyu.A watan Mayu ya kulla wata yarjejeniya ta shekara biyu da Chelsea, kuma a yanzu ya bar kungiyar mako biyar bayan Frank Lampard ya koma kungiyar a matsayin kociya.

An haramta wa Chelsean sayen sabbin 'yan wasa har zuwa watan Janairu na 2020, sakamakon binciken da aka yi kan sayen 'yan wasa na waje da suka yi 'yan kasa da shekara 18.

Yanzu 'yan wasan baya da Chelsea take da su bayan tafiyar Luiz da kuma Gary Cahill wanda ya koma Crystal Palace a karshen kakar da ta wuce, sun hada da Antonio Rudiger, na Jamus, da Kurt Zouma, wanda a kakar da ta wuce yana zaman aro a Everton,da kuma Andreas dan Denmark.

Arsenal za ta fara kakar Firimiya ta bana a Newcastle ranar Lahadi, yayin da Chelsea za ta ziyarci Manchester United.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment