Wednesday, 7 August 2019

Bauchi: An rufe jami'ar ATBU bayan gada ta rufta da dalibai

Wata gada ta rushe, har ta yi sanadiyyar rasuwar dalibai uku da ke karatu a jami`ar fasaha da ke jihar Bauchi.


Wannan al'amarin dai ya fusata daliban, wadanda suka yi bore ta hanyar farfasa wasu gine-ginen da ke cikin jami`ar.

Tuni dai mahukunta suka rufe makarantar domin kwantar da rikicin.

Gadar dai, karama ce ta karfe da ke taka rawa a matsayin kadarko da ke hada wasu tsangayoyi da wurin kwanan dalibai da ke sabon matsugunin jami`ar na Gubi.

Kuma ta karye ne sakamakon cinkoson da dalibai suka yi a kanta, bayan wani mamakon ruwan sama da aka tabka.

Wannan lamari dai ya hassala daliban makarantar, musamman ma yadda wata ruwayar ta nuna cewa wasu daga cikin daliban da suka jikkata sun garzaya asibitin jami`ar, amma a cewarsu ba su samu jami`an lafiya da isasshen maganin da za a duba lafiyarsu ba.

Ga shi kuma suna rubuta jarrabawa! Don haka sai suka shiga farfasa wasu muhimman abubuwa da ke cikin makarantar.

Mahukunta a jami`ar sun tabbatar da faruwar hadarin.Farfesa Muhammad Ahmad Abdulaziz shi ne shugaban jami`ar fasaha ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi:

Ya bayyana cewa hukumar jami`ar ta dade da yunkurin gina gadar, amma abin ya gagara, sakamakon kalubalen da take fuskanta ta fuskar kudi, tun kafin ya zama shugaban jami`ar, amma yanzu za su kukuta su ga sun gina gadar.

A halin da ake ciki dai shugaban jami`ar ya bayyana cewa da wuya su san yawan daliban da wannan hadari ya rutsa da su.

Sai bayan 'yan kwana-kwana da sauran jami`an da abin ya shafa sun kammala aikin da suke yi na ceto.

Kazalika hukumar jami`ar ta tsai da ranar 19 ga wannan watan Agusta domin sake bude jami`ar, kuma nan da wannan lokacin ne suke sa ran karbar cikakken rahoto a kan abin da ya jawo yamutsin da daliban suka yi, da hanyoyin kauce masa a nan gaba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment