Saturday, 24 August 2019

Chelsea ta yi nasara a karon farko karkashin jagorancin Lampard bayan data lallasa Norwich da ci 3-2: karanta bayanan da suka shafi wasan

A karin farko kungiyar Chelsea karkashin jagorancin sabon me horas da ita kuma tsohon dan wasanta, Frank Lampard ta yi nasara a wasan data buga a gasar Premier League inda ta lallasa Norwich City da ci 3-2.
Wasan da aka buga da Ranar Yau Asabar ya karewa Chelsea cikin jin dadi inda ta lashe duka maki 3n wasan.

Tammy Abraham ne ya fara ciwa Chelsea kwallo ana mintina 3 da fara wasa saidai Cantwelll ya ramawa Norwich kwallon mintuna 6 kacal da wasan, Mount ya kara saka Chelsea cikin farin ciki bayan da ya ci mata kwallo ta 2 ana cikin mintuna 17 da wasa, saidai murnar su ta koma ciki bayan da Pukki ya farke kwallon ta Mount cikin mintuna 30 da wasa.

Haka aje hutun rabin lokaci da sakamakon 2-2.

Saidai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Tammy Abraham ya kara ciwa Chelsea kwallo ta 3 wadda itace ta makale har aka tashi wasan a haka da sakamakon 3-2.

Tammy Abraham dan shekaru 21 ya kafa tarihin kasancewa dan kwallon Chelsea mafi karancin shekaru na 3 daya taba ci mata kwa─║laye 2 a wasa daya a gasar Premier League.

Bayan wasan ya bayyana cewa, wannan abunda yayi dama abinda yake ta mafarkin yine wa kungiyarshi ta Chelsea.

Shima dan wasan Norwich City Teemu Pukki ya kasance dan wasan Premier League na 10 daya jera wasani 3n farko na gasar Premier League yana cin kwallaye sannan kuma ya kafa tarihin kasancewa dan wasa na 2 daya ci kwallaye 5 a wasanni 3 na farko na gasar Premier League.

Pukki ya ci Liverpool kwallo 1 a wasan da suka buga sannan kuma ya ci Newcastle kwallaye 3 sai kuma yau da yaci Chelsea kwallo 1

Saidai masu sharhi na ganin har yanzu Chelsea na da matsala ta wajan masu tsaron bayanta abinda ya kamata ace ta dauki mataki akai kenan idan tana son ci gaba da samun nasarori irin wannan nan gaba. Yanzu dai Chelsea ta koma matsayi na 12 akan teburin Premier League.

Pedro da a farko aka tsara cewa yana cikin wanda zai bugawa Chelsea wasa ya samu rauni wanda hakan yasa be buga mata wasan na yau ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment