Saturday, 24 August 2019

Cutar tabar laturoni ta barke a Amurka

Jami'an kula da lafiya a Amurka sun ce wani maras lafiya ya mutu bayan da ya kamu da cutar numfashi mai tsanani saboda shan tabar laturoni da yake yi,


Mutuwar ta sa mutumin kusan ya zama na farko a Amurkar da ya gamu da ajalinsa a sanadiyyar kamuwa da cutar huhu, ta dalilin shan wannan taba ta zamani.

Ma'aikatar lafiya ta jihar Illinois ta Amurkar, ta ce marigayin wanda ba a bayyana sunansa ba, dan tsakanin shekara 17 da 38 ne.Jami'an lafiya a jihar sun kara da cewa an kwantar da wasu mutane 22 da suka ce sun yi amfani da tabar ta lautroni a asibiti, a makon da ya wuce.


Wakilin BBC ya ce: '' Akalla mutane biyu ne suka mutu a Amurkar bayan da sigarinsu ta laturoni ta tarwatse a fuskarsu, amma wannan ka iya kasancewa mutuwa ta farko ta sanadiyyar cutar da ke da alaka da shan tabar laturonin.''

Mutuwar mutumin ta kasance ne yayin da ake samun barkewar cutuka a Amurkar, wadanda jami'an lafiya ke dangantawa da shan sigarin ta laturoni.


A ranar Laraba hukumar yaki da yaduwar cutuka ta kasar ta ce, kusan mutane 150 ne a Amurkar suka kamu da rashin lafiyar da ke da nasaba da zukar tabar ta laturoni, kuma tsananin alamun cutar na da tayar da hankali.

Hukumar ta ce tana gudanar da bincike kan abin da ta kira tarin cutukan huhu a fadin kasar, wadanda ke da dangantaka da shan tabar ta zamani.


A sama da wata biyu da ya gabata an samu mutane kusan 200 a jihohi 22 na Amurkar da suka je asibiti, yawancinsu matasa ne da 'yan shekara goma sha wadanda ke fama da tsananin cutar numfashi. Babu tabbas ko cutukan nasu suna da alaka da juna.

Jami'ai sun ce ba a ga alama kamar ko cutukan masu yaduwa ba ne daga mutum zuwa mutum. Yawanci dai ana ganin shan tabar laturoni ya fi rashin illa kan shan taba sigari da ake kunna wa wuta, sai dai kuma ba a san illar ita tabar ta laturoni ba ta can gaba.
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment