Sunday, 4 August 2019

Da wuya Idan Real Madrid zasu iya sayena>>Pogba

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na neman zunzurutun kudin da suka kai fan miliyan 150 akan tauraron da wasansu, Paul Labile Pogba da suka siyo daga Juventus akan fan miliyan 89 shekaru 3 da suka gabata.


Idan Real Madrid ta sayi dan wasan zata rika biyanshi albashin fan dubu dari 5 duk sati, watau fan miliyan 26 kenan a shekara.

Pogba na neman Madrid ta bashi kwantirakin buga mata wasa na shekaru 4, hakan na nufin zasu kashe fan miliyan 104 kenan a tsawon lokacin da zai mata wasa.

Wakilin Pogba, Mino Raiola na neman a biyashi kudin aiki da suka kai kashi 10 na kudin cinikin Pogba da zasu kai fan miliyan 15.

Gaba daya Madrida zasu kashe fan miliyan 270 kenan akan Pogba.

Abinda shugaban kungiyar, Florentino Perez yake shakkun aikatawa, musamman a yanzu da kungiyar ke neman raba gari kocinta, Zinedine Zidane bayan da yayi rashin nasara a wasan sada zumunta da suka buga da Atletico Madrid da ci 7-3.

Madrid na tunanin sake kawo tsohon kocinta, Jose Mourinhine, kamar yanda Mirror Uk ta ruwaito, idan kuwa haka ta faru to Komawar Pogba Real Madrid ta sha ruwa kenan ganin cewa shi da Mourinho basa shiri.

Pogba na kokarin yin duk me yiyuwa dan ganin ya bar Man United zuwa Real Madrid inda har a jiya yaki zuwa wasan sada zumunta da Man U din ta buga da AC Milan bisa wai bashi da lafiya amma a zahiri yana shirin ganin barin kungiyarne kamin kulle kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa a ranar Alhamis me zuwa.

Saidai wasu rahotanni sun ce kocin Man U, Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar da cewa Pogba zai ci gaba da zama a kungiyar.
Saidai a yau, Lahadi Pogba ya sake sakin wani sako a shafinshi na sada zumunta dake nuna cewa zai bar Manchester United. Saidai yayi gaggawar cire rubutun nashi watakila dan kada yayi tunanin cewa yana nufin barin kungiyar.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment