Thursday, 8 August 2019

Dalibai 30 ne suka taru suna daukar hotob Selfie shiyasa gadar jami'ar Bauchi ta rushe>>Shugaban jami'ar


A yayin ziyarar da wakilan Gwamnatin jihar Bauchi suka kai jami'ar ATBU dan ganin yanda lamarin rugujewar gada da yayi sanadiyyar mutuwar dalibai 3 ya auku, shugaban makarantar, Muhammad Abdullazeezya bayyana yanda lamarin ya wakana.Yace ba kamar yanda ake yayatawa ba cewa dalibai 7 ne suka rasu, dalibai ukune suka rasu biyu mata daya namiji, biyu daga jihar Kogi daya kuma daga jihar Benue.

Yace sun gina gadar karfenne tsakanin dakin kwanan dalibai da dakunan karatu wadda a lokaci guda mutane 10 zuwa 15 ne zata iya dauka kuma ba'a yita dan a tsaya a kanta ba, an yi tane kawai dan a hau a wuce.

Yace amma ranar da wancan ibtila'i ya faru, an yi ruwa yana ta hankoro sai wasu dalibai 2 suka zo wucewa, sai suka ga gurin ya musu kyau da daukar hoto, shine suka tsaya kan gadar suna daukar hoto, a haka a haka har suka kai kusan su 30.

Suka tare gadar babu hanyar wucewa shine lodi ya mata yawa ta ruguje.

Shugaban makarantar ya yabawa gwamnati da jami'an tsaro da suka bada gudummuwa akan lamarin sannan yace sun kafa kwamiti da zai binciki ainahin yanda lamarin ya faru.

Gwamnatin Bauchi ta sha alwashin gyara gadar data rushe.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment