Wednesday, 14 August 2019

Dalilin da yasa nafi Messi>>Ronaldo


Cristiano Ronaldo Ya bayyana dalilin da yasa yafi Messi
Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa ya bayyana abokin takararshi na kungiyar Barcelona, Lionel Messi a matsayin gwanin dan kwallo wanda Duniya zata rika tunawa dashi saboda kwarewarshi amma yace shi kuma daukar kofuna da yayi da kungiyoyi daban-daban ne abinda ya banbantashi da Messi.

"Messi babban dan wasane da za'a rika tunawa dashi ba kawai dan kyautukan Ballon d'Or din da ya ci ba, harma saboda kwarewar da ya nuna wajan kasancewa na daya a koda yaushe kamar yanda nima nike, banbancina dashi shine na yi wa kungiyoyi daban-daban kwallo kuma na dauki kofin Champions League da kungiyoyi daban-daban" kamar yanda Ronaldo ya gayawa DAZN.

Ronaldo ya bayyana cewa 'yan kwallon da suka lashe kyautar Ballon d'Or sau 5 basu da yawa dan nakejin cewa ina son kalubale, inji Ronaldo.

A shekarar 2008 ne Ronaldo ya lashe kofin Champions League a karin farko da kungiyar Manchester United sai kuma a shekarun 2014, 2016, 2017 da 2018 da ya sake lashe kofin a kungiyar Real Madrid.

Da yake bayyana yanda ya kasance da kuzari kuma na gababa duk da yake cewa shekarunshi sun fara ja, Ronaldo ya bayyana cewa kuzarin da yake dashi abune da bawai haka kawai a sama ya sameshi ba. Kullun ina zuwa motsa jiki da kuma samun horo akan yanda zan yi nasara bawai samun kudi ba kawai,banda matsalar kudi, abinda ke raina shine yanda zan kafa muhimmin tarihi a Duniyar Kwallo, Inji Ronaldo.   


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment