Pages

Sunday 11 August 2019

Dan bindiga ya bude wa masallata wuta a Masallaci a Norway

An cafke wani mutum a Norway wanda ya bude wuta a Masallaci a ranar Asabar.
'Yan sanda sun ce dan bindigar ya bude wuta ne a Masallacin wata cibiyar nazarin addinin Islama a wajen Oslo babban birnin kasar.


Matashin wanda aka bayyana a matsayin dan kimanin shekara 20, dan asalin kasar Norway ne, kuma 'yan sanda sun ce sun gano gawar wata mata a gidansa, da ake tunanin 'yar uwarsa ce.

'Yan sanda sun ce shi kadai ya kai harin a masallacin.

Daraktan masallacin ya shaida wa kafofin yada labaran yankin cewa wani dan shekara 75 ne ya samu rauni a lokacin da dan bindigar ya kai harin.

"Wani farar fata sanye da kaki da hular kwano ya harbi daya daga cikin mambobinmu," kamar yadda Irfan Mushtaq ya shaida wa jaridar Budstikka.

Ya kuma shaida wa wata kafar talabijin ta TV2 cewa dan bindigar ya bude wuta ne dauke da bindigogi guda biyu, kafin 'yan sanda su isa wurin.

Wasu majiyoyi na 'yan sanda sun shaida wa kafar yada labarai ta NRK cewa an samu makamai a masallacin da ke garin Baerum, bayan harin.

Masallacin dai ya kara daukar matakan tsaro bayan harin da wani dan bindiga ya kashe mutum 51 a masallatai biyu a Chrischurch, a New Zealand, a farkon shekarar 2019, kamar yadda kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ruwaito.
BBChausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment