Sunday, 4 August 2019

Dan Bindiga ya kashe gwammman mutane a Amurka

Wani dan bindiga ya harbe gomman mutane har lahira a wani shago da ke birnin Texas na Amurka.


Harin ya auku ne a shagunan Cielo Vista Mall da ke El Paso, kilomita kadan daga iyakar Amurka da kasar Mexico.

Akwai kuma akalla mutum 22 da aka kai asibiti domin duba raunukan da suka samu a sanadiyyar harbin da dan bindigan yayi musu.

An kama wani mutum, amma jami'an 'yan sanda sun ce suna ganin mutumin shi kadai ya kai harin, amma kakakin rundunar 'yan sandan bai iya bayyana yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Saje Robert Gomez ya ce: "Ba za iya bayyana muku komai ba sai bayanmun tabbatar da sahihancin alkaluman da ke gaban mu.

An dai fara samun rahotannin harin ne da misalin karfe 11:00 na safiya (wato karfe 7 na yamma agogon Najeriya).Wani irin martani ya biyo bayan harin?

Magajin garin El Paso, Dee Margo ya bayyana harin a matsayin "wanda ban taba tsammanin zai iya aukuwa a wannan yanki namu ba. Abin ya girgiza ni".

Shugaban Amurka Donal Trump ya ce rahotannin harin da ya samu sun ce "lamarin babu kyaun ji, kuma ya kashe mutane masu yawa."
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment