Monday, 12 August 2019

DIREBAN SARKIN KEFFI YA TSINCI DALOLIN MANIYYACI YA MAYARWA DA MAI KUDIN

An karrama Ibrahim Suleiman Direban Sarkin Keffi, bayan ya yi tsintuwar kudin wani Alhaji kuma ya bayar da kudin ga hukumar Alhazai don a yi cigiya ga mai su, rahoton na hukumar Alhazai, bai bayyana adadin kudin da ya tsinta a Dalar Amurka ba, Amman ance kudin suna da yawa.


The Nasarawa State Amirul hajj for 2019 HRH JSC Rt Sidi Dauda Bage has rewarded pilgrim from Nasarawa state Ibrahim Abdulahi Suleiman for returning a missing dollars to officials of the board in Saudi Arabia.

La'akari da halin kwarai da Ibrahim Abdullahi Suleiman ya nuna yasa Mai martaba Sarkin lafia Tsohon Mai Sharia Sidi Dauda Bage, Wanda shine Amirul Hajj na 2019 a jihar Nasarawa ya karrama shi da kayauta mai tsoka a kasa mai tsarki, inda ya bayyana shi a matsayin Mai Gaskiya kuma  Nagari Abin Koyi.

Sarkin lafia Sidi Bage ya yi kira da sauran Alhazan jihar Nasarawa da Najeriya baki daya da su yi koyi da halin gaskiya a duk inda suke kuma su zama jakadu kwarai.

Alhajin da ya yi tsintuwar Ibrahim Abdullahi Wanda ya bayyana kansa a matsayin Mai tuka sarkin keffi ya yi gadiya game da karrama shi da kyauta da aka yi.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment