Saturday, 10 August 2019

EFCC ta soma bincikar gwamnatin Obasanjo kan salwantar kudin lantarki


media
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta soma bincike kan shirin samar da wutar lantarkin da ya lakume dala biliyan 16 a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo.

Majiyoyin hukumar ta EFCC kamar yadda wasu jaridun kasar suka rawaito, sun ce za a tuhumi wadanda suka jagoranci ayyukan shirin samar da lantarkin a lokacin shugabancin na Obasanjo, zalika binciken zai kuma fadada zuwa kan yan kwangilar da suka gudanar da ayyukan lantarkin a zamanin gwamnatocin marigayi Umaru Musa Yar’Adua da kuma Goodluck Jonathan.
Hukumar ta EFCC za ta kuma tuhumi wasu tsaffin ministocin Najeriya biyu da ba’a bayyana sunayensu ba, da kuma wasu tsaffin manyan jami’an gwamnatin kasar 18, da na babban bankin kasar CBN.
A karshen watan Yuli, majalisar wakilan Najeriya ta cimma matsayar gudanar da bincike dangane da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta biya kan kwangilolin magance matsalar rashin tsayayyar hasken lantarki a kasar.
Majalisar ta ce za a binciki tsohuwar gwamnatin da Olusegun Obasanjo ya jagoranta daga 1999 zuwa 2007, don bada bahasi kan dala biliyan 16 da gwamnatin yai ikirarin kashewa kan inganta wutar lantarkin.
A waccan lokacin, tsohuwar gwamnatin ta ce zuba makudan kudaden a fannin lantarkin zai samarwa da Najeriya karfin wutar da zai kai Megawatts dubu 40 a shekarar 2020.
Har yanzu dai samar da hasken lantarki batu ne da ‘yan siyasar Najeriya ke amfani da shi wajen neman kuri’a yayin yakin neman zabe, duk da ikirarin gwamnatocin da suka gabata, na zuba makudan kudade a fannin, ba tare da an ga sahihin sakamako ba.
RFIhausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment