Tuesday, 6 August 2019

Ganduje ya bai wa kowanne dan wasan Pillars dala 1,000

Gwamnan jihar Kano ya bai wa kowane dan wasan Kano Pillars da suka lashe kofin Aiteo kyautar dala 1,000 (naira 360,000) sakamakon rawar-ganin da suka taka.


Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya karbi bakuncin 'yan wasan bayan sun isa Kano daga Kaduna a karon farko tun lokacin da suka lashe kofin, ya ce wannan kyauta ce ta kashin kansa kamar yadda ya yi musu alkawari.

Mai magana da yawun kulob din Lurwanu Malikawa ya shaida wa BBC cewa kudin da gwamnan ya bayar cika alkawarin da ya yi ne lokacin da ya gana da 'yan kwallon a Kaduna kafin wasan karshe da suka yi da Niger Tornadoes.


Ya kara da cewa akwai wasu kyatuttukan da 'yan wasan za su samu daga gwamnati.


Shekera 60 aka shafe rabon da wani kulob a Kano ya dauki wannan kofi, a don haka Ganduje ya ce "wajibi ne a yi murna sannan zai yi duk abin da ya dace wurin tallafawa kulob din".

Gwamnan ya ce za shirya wa 'yan wasan "liyafa ta musamman domin karrama su bisa wannan nasara da suka smau".

A ranar Asabar ne Pillars za ta fafata da Ashante Kotoko na Ghana a wasan kifa-daya-kwala na gasar cin kofin Zakarun Afirka ta bana.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment