Thursday, 8 August 2019

Garin da ba maza sai mata

Magajin garin Miejsce Odrzanskie, wani kauye a kudancin Poland ya yi alkawarin bai wa duk ma'auratan da suka haifi da namiji gagarumar kyauta.


Wakiliyar BBC, Mike Sanders ta rawaito cewa an kwashe kimanin shekaru 10 da aka samu wasu ma'aurata da suka haifi da namiji Mike Sanders.

Shi dai wannan gari mai suna Miejsce Odrzanskie ba sananne ba ne, inda yawan gidajen garin ba su wuce guda 100 ba. Sai dai garin na da yawan gandu da ciyayi gwanin sha'awa ga tashin kananan yara.

Abin da kawai yake ci wa garin tuwo a kwarya shi ne yawan mata da karancin yara maza.
Halin damuwar da mutanen garin suke ciki ta fito ne bayan da 'yan matan garin suka fara matsa wa masu aikin kashe gobara na garin nasu da su koya musu aikin.

Hakan ne ya sa 'yan matan suka kafa wata kungiyar masu kashe wuta, al'amarin da ya ja hankalin 'yan jarida.

Yanzu dai magajin garin na Miejsce Odrzanskie, Rajmund Frischko ya ce duk ma'auratan da suka haifi da namiji za su rabauta da gagarumar kyauta sannan kuma za a sanya wa daya daga cikin bishiyoyin garin sunan dan.

Batun haihuwa dai a nahiyar Turai wani abu ne da yake kara yin karanci, ta yadda ma'aurata kan zabi haihuwar da guda kacal ko biyu ko uku.

A wasu lokutan ma namiji da mace kan zabi rashin haihuwar kwata-kwata.

Har wa yau, a kan samu yanayin auren jinsi guda da hakan ba zai samar da haihuwa ba.
BBCHausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment