Pages

Saturday 24 August 2019

Gwamna Wike Ya Rushe Masallaci Mafi Girma A Jihar Ribas

Shugabannin al'ummar Musulmi a PortHarcourt, babbar birnin jihar RIvers, sun yi Allah wadai da rusa babban Masallacin Trans-Amadi, inda suka yi kira da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo dauki.


Limanin Masallacin, Haroon Mohammed, ya ce ma'aikatan gwamnatin karkashin umarnin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ne suka dira Masallacin da 'yan sanda ranar 20 ga watan Agusta domin rusawa.

Ya ce sun yi ikirarin cewa ginin Masallacin bai cikin tsarin gine-ginen jihar RIvers alhalin gwamnatin jihar ce ta tabbatarwa Musulmai filin domin gini a baya.

Yayin da yake kira ga gwamna Nyesom Wike, Imam Haroon ya ce: "Wannan shine Masallaci mafi girma. Musulman duniya su shaida cewa gwamnatin jihar ce ta ba mu damar gina Masallacin. 

Sau uku kenan ana cin mutuncinmu. An fara ranar 29 ga watan da ya gabata, sannan ranar 16 ga Agusta, sai 20 ga wata ba tare da wani sanarwa ba."

"Yau an hanamu wajen ibada, Bamu son tayar da wani rikici da ma'aikatan gwamnati. Muna son duniya ta rokan mana gwamna ya bamu wajen Ibada, saboda babban Masallacin nan ne daya tilo da al'ummar Trans-Amadi ke amfani da shi."

Gabanin yanzu, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya jaddada cewa jiharsa ba jihar Musulmai bace, jihar Kiristoci ce kuma babu wanda ya isa ya hanashi abinda yaga dama.

Majalisar koli ta shari'ar addinin Musulunci NSCIA ta yi tsokaci kan wannan magana da gwamnan yayi a lokacin inda take jawo hankalinsa cewa a matsayinshi na shugaba, bai kamata ya rika magana irin haka ba.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment