Thursday, 8 August 2019

Gwamnatin Kaduna Ta Gindaya Sharuddan Jinyar El-Zakzaky


Sheik El-Zakzaky
Gwamnatin ta ce duk da yake dai ba muzgunawa Mal. El-zazzaky ta ke son yi ba, akwai bukatar shimfida ka'idoji kafin wadanda ake karar su fice zuwa Indiya.


Gwamnatin ta gindaya ka’idoji bakwai da tace tilas a cika kafin barin El-Zakzaky da mai dakinsa su tafi jinya. Na farko gwamnatin tace, tana so gwamnatin tarayyar Najeriya ta binciko ko asibitin ya yi shirin karbar jinyarsa da kuma tabbatar an kiyaye ka’idojin jinyar. Banda haka kuma sai masu jinyar sun dauki alkawarin cewa, zasu dawo Najeriya idan aka sallame su daga asibiti, kuma sune zasu dauki nauyin dukan dawainiyar tafiyar da kuma jinyarsu.
Wasu daga cikin sharuddan da gwamnatin jahar Kaduna ke son a shimfada wa sheikh El-zazzaky da mai-dakin shi kafin fita Indiya neman lafiyar dai sun hada da kawo babban sarki Mai daraja ta daya, da kuma sanannen mutum da za su tsaya musu Ana kuma bukata Mal. El-zazzaky da mai-dakin da lauyoyin su su dauki rantsuwa cewa da sun sami lafiya za su dawo Nigeria, sannan kuma za a hada su da jami'an tsaro na gwamnatin tarayya su zauna da su har zuwa ranar da za su dawo gida Najeriya.
Har wa yau, gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci ofishin jakadancin Najeriya a kasar India ta sa ido sosai ta kuma tantance duk wanda ya nemi ganin wadanda ake tuhuman, banda haka kuma ya kasance babu wanda zai iya ganinsu sai da izinin ofishin jakadancin Najeriya.
VOAhausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment