Thursday, 8 August 2019

Hazard ya ciwa Madrid kwallo ta farko


Red Bull Salzburg vs Real Madrid live online: friendly match
A karshe dai sabon dan wasan Real Madrid data siyo daga kungiyar Chelsea, Eden Hazard ya ci mata kwallo a wasan da Madrid din ta buga da kungiyar Salzburg inda aka tashi wasan 1-0.

Ana mintuna 19 da wasa Hazard yayi mamaya ya buga kwallo daga tazara me dan nisa kuma ta shiga raga, wannan kwallo ce ta makale har aka tashi.

Bayan wasan, Hazard ya bayyana cewa yayi ta jiran irin wannan dama kum yau gashi Allah yasa ya cima burinshi, yace amma kada a manta wannan wasan sada zumuntane kawai, nan da 'yan kwanaki zasu fara wasannin Laliga wanda suna samun kwarin gwiwar yin nasara akai.

Wannan ne karo na biyu a jere da Real Madrid ta yi nasara a wasannin sada zumuntar data buga bayan ta yi fama da rashin nasara a baya, ciki hadda wasan da abokiyar takararta, Atletico Madrid ta cita 7-3.

Wani abu daya kara jan hankali a wasan shine rashin saka Bale da Zidane yayi inda ake ganin cewa da gaske Zidane yake ba zai yi wasa dashi ba a kaka me zuwa.

Sau biyu Zidane ya saka Bale a wasannin kakar sada zumunta 5 da sukayi wanda shima canjine.

Zidane dai na son sayar da Bale dan kawo Erikson da Pogba saidai Shugaban Madrid, ya hana Bale din tafiya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment