Tuesday, 6 August 2019

Indiyawa na murnar zuwan Zakzaky kasarsu neman magani

Tun bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta bai wa jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa, damar tafiya kasar Indiya domin neman magani, wasu Indiyawa suka "fara" murna da zuwan na sa.


Sun kirkiri wani maudu'i a shafin Twitter na #IndiaWelcomesZakzaky da ke nufin India na maraba da Zakzaky.

A safiyar ranar Litinin ne dai kotun ta bai wa mutanen biyu damar zuwa kasar ta Indiya domin neman magani, kamar yadda lauyoyinsa suka nema.

Damar da babbar kotun ta Kaduna ta bai wa Sheikh Ibrahim Zakzaky ta fita kasar waje tana tattare da wasu sharudda da kotun ta ce lallai sai an cika su.

Daya daga cikin sharuddan shi ne dole ne jami'an gwamnati su yi wa Zakzaky da matarsa rakiya zuwa Indiya.

Tun bayan kama shi a Disambar 2015, Indiyawa mabiya Shi'a sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashe musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Tekun Fasha, wurin nuna goyon baya a gare shi a shafukan saza zumunta.

Wannan ne ya sa wasu 'yan Indiya suke ta faman murna cewa mutumin da suka dade suna fafutukar neman a saki, yanzu zai je kasarsu domin neman magani.Ga abinda wasu indiyawa ke cewa akan zuwan Zakzaky kasar:
Wannan cewa yake muna yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kammala duk mai yiwuwa wajen ganin Zakzaky da mai dakinsa sun zo India domin neman magani.
Shi ma wannan yana cewa India na yi wa Zakzaky maraba. Kotun Najeriya ta bai wa Zakzaky da mai dakinsa damar zuwa India neman magani.

Mene ne hadin Zakzaky da 'yan India?

Tun kafin bai wa Zakzaky damar fita Indiya neman magani, wasu 'yan kasar sun dade suna fafutukar neman a saki malamin na Shi'a ta hanyar shafukan sada zumunta.

Hakan ya sa wasu tunanin mece ce alakar Zakzaky da kasar ta Indiya.

Ana ganin kasancewar Indiya wata kasa da yanzu haka a duniya ta yi fice a fannin kiwon lafiya, inda mutane daga sassa daban-daban na duniya ke tururuwa domin neman magani, ya sa shehun malamin ko kuma jama'arsa suka zabi Indiyar domin neman lafiya.

Har wa yau, kasar India na daya daga cikin kasashen da ba na Musulmi ba, amma masu yawan mabiya mazhabar Shi'a a duniya, inda bayanai suka ce akwai 'yan Shi'a da dama a Musulman kasar.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment