Thursday, 8 August 2019

Inter Milan ta sayi Lukaku daga Man United


Romelu Lukaku
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta sayi dan wasan kasar Belgium, Remolu Lukaku daga kungiyar Manchester United akan Fan miliyan 74.

Dan shekaru 26 ya ciwa Manchester United kwallaye 42 a wasanni 96 da ya buga mata a shekaru 2 da ya shafe a kungiyar bayan zuwanshi daga Everton akan fan miliyan 75.

A yanzu Lukakune dan wasa na uku mafi tsada da aka siya a gasar Seria A bayan Ronaldo da Juventus ta siya akan fan miliyan 99.2 da kuma Gonzalo Higuain akan fan miliyan 75.3.

Da yake hira da manema labarai Lukaku ya bayyana cewa Inter ce kungiya daya tilo dake ranshi.

Na zone in dan in sake daukakasu zuwa sama, injishi kamar yanda BBC ta ruwaito.
 

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment