Monday, 5 August 2019

Iran ta sake kwace wata tankar mai a tekun Fasha

Rahotanni daga Iran sun bayyana cewa kasar ta sake kwace wata tankar dakon mai a tekun Fasha mallakin kasashen ketare wanda ke matsayin tanka ta 3 da kasar ta kwace cikin wata guda abin da ke kara tsamin alaka tsakaninta da babbar abokiyar dabinta Amurka.
Wata sanarwa daga Rundunar kare juyin juye halin Iran ta ce dakarunta sun kwace wannan jirgi mai dauke da kimanin lita dubu dari 7 na man fetur da aka yi fasakaurinsa, sanna ta kama ma’aikatan jirgin ‘yan kasashen waje su 7.

Zaman tankiya tsakanin kasashen biyu da ke zaman doya da manja ya dada kamari ne a wannan shekarar, bayan Amurkan ta zafafa matsin lamba kan Iran.

Tun a watan Mayu, an kaiwa jiragen ruwa hari, an kabe jirgi mara matuki tare da kwace tankunan mai, shekara daya bayan Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliya da aka kula tsakanin Iran da wasu manyan kasashen duniya, sannan ta fara sanya takunkumai masu gauni kan Iran din.

Kwacen tankan mai da Iran ta yi na baya bayan nan dai shi ne na uku a kasa da wata guda a tekun Fasha, inda ta nan ne akasarin danyen man duniya ke ratsawa don isa ga abokan hulda.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga shaida ko jirgin ruwan wace kasa Iran ta kwace ba, haka zalika inda ma’aikatan cinsa da ta kama suka fito, ita ko Birtaniya cewa ta yi babu wani jirgi mallakanta da baya karkashin ikonta a halin yanzu, kuma babu dan kasarta cikin ma’aikatan jirgin da aka kama.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment