Sunday, 25 August 2019

Isra'ila ta kaiwa kasar Iran hari

Isra'ila ta ce ta kai wa wani wurin sojin kasar Iran a kasar Syria hari da manufar dakile yunkurin da Iran din ke yi na kai musu hari da jirage maras matuka.


Ba kasafai ba dai rundunar sojin Isra'ila ke bayyana ayyukansu a kasar Syria, to amma ta yi ikrarin kai harin sama ranar Asabar wanda ta ce ta kai kan 'jiragen Iran maras matuka masu kisa'.

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jinjina wa kokarin sojojin nasa na kai hari.

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Netanyahu ya ce "Ina jaddada cewa Iran ba ta da garkuwa a kowane wuri. Sojojinmu na ko'ina domin yakar zaluncin Iran. Kashe makashinka kafin ya kashe ka."An dai yi amannar cewa Isra'ila ta gudanar da daruruwan hare-haren sama a Syria, tun bayan barkewar yakin basasa a kasar a 2011, da manufar hana kasar Iran samun wurin zama a Syria.

Mai magana da yawun sojin kasar ta Isra'ila, ya ce sun kai harin ne a kudu maso gabashin birnin Damascus na Syria.

Wasu majiyoyin sojojin kasar Syria da kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito na cewa sojoji sun dakile wasu jiragen yakin sama a tsibirin Golan a yunkurinsu na dosar birnin Damascus.

Wasu rahotanni sun ce jirage maras matuka mallakar Isra'ila sun sauka a wani sansanin 'yan kungiyar Hezbollah da Iran ke mara wa baya, a Beirut babban birnin kasar Lebanon.

Sai dai jagororin kungiyar Hezbollah sun ce wani jirgi maras matuki ya fado kan soron cibiyar watsa labaransu, inda jirgi na biyu shi kuma ya fashe a sama ya kuma fado kusa da ginin nasu.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment