Saturday, 10 August 2019

Jami'ar Bayero dake Kano ta kori dalibai 24 dake shekarar Karshe


Jami'ar Bayero dake Kano ta sallami dalibanta dake shekarar karshe su 24 daga makarantar kamar yanda hukumar makarantar ta bayyana a jiya, Juma'a 9 ga watan Augusta.


Me magana da ywun makarantar, Lamara Garba ya shaidawa manema labarai cewa jami'ar ta kori dalibai 6 da suka gabatar da sakamakon bogi da kuma wani dalibi da ya gabatar da da sakamakon NECO da aka soke., kamar yanda Premiumtimes ta bayyana,

Sanarwar da jami'ar ta fitar ta bayyana cewa, saidai sauran dalibai 18 za'a sake basu damar tantancewa a karo na biyu kan takardun da suka gabatar na shiga jami'ar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment