Wednesday, 7 August 2019

Jami'ar Bayero ta samu lasisin bude gidan talabijin

Hukumar kula da kafafen yada labaru ta Najeriya, NBC, ta bai wa jami'ar Bayero da ke Kano lasisin da zai ba ta damar kafa gidan talabijin.


Wannan lasisi da jami'ar ta samu zai ba ta damar kafa gidan talabijin na kanta ta yadda za ta rinka koyar da dalibai aikin yada labaru na talabijin, a cewar shugaban hukumar ta NBC Ishaq Kawu.

Shugaban na NBC dai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jami'ar ta Bayero da ke Kano.

Yanzu haka dai jami'ar tana da gidan rediyo wanda ke yada labaru daga harabarta.

Shugaban bangaren karatun gaba da digiri na jami'ar Farfesa Umar Pate ya shaida wa BBC cewa sun samu tallafin kudaden gina dakin gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin din daga wasu kungiyoyi.

Farfesan, wanda shi ne ya jagoranci sake gina gidan rediyon da samar masa da kayan aiki na zamani, ya ce nan gaba za a fara aiki domin gina gidan talabijin din.Shugaban jami'ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce wannan lasisi zai bunkasa harkar yada labaru a Najeriya.

Ya kara da cewa za a yi amfani da lasisin wajen horas da dalibai aikin jarida na binciken kwakwaf.

Jami'ar Bayero na daga cikin jami'o'in da suka yi fice a fannin koyar da aikin jarida a kasar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment