Wednesday, 28 August 2019

JAM’IYYAR APC TA NADA GWAMNAN JIGAWA A MATSAYIN SHUGABAN ZABEN FIDDA GWANI A JIHAR KOGI

Jama’iyyar APC ta kasa ta nada Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a matsayin shugaban gudanar da zaben fidda gwani na neman kujerar Gwamna da za’ayi a Jihar Kogi.


Gwamnan wanda a safiyar jiya  ya tashi daga filin Jirgi na Malam Aminu Kano domin ya isa birnin tarayya Abuja, inda daga nan zai garzaya izuwa jihar kogi don ya gabatar da aikin da Jam’iyya ta dora masa.

Gwamnan ya tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Gandujeda kuma sauran manya da zasu raka domin ya sauke nauyin dake kansa.

Ba wannan bane karon farko da Gwamna Badaru Abubakar yake samun irin wannan karamci daga uwar jam'iyyar APC ba, Domin ko a baya sai da ya jagoranci irin wannan kwamati a jihar Ondo.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment