Pages

Friday 23 August 2019

Ji Martanin sanata Dino Melaye bayan da kotu ta soke zabenshi


Bayan da kotun sauraren kararrakin zabe dake da zama a Lokoja jihar Kogi ta soke zaben sanata Dino Melaye a matsayin sanatan mazabar Kogi ta yamma, Sanatan ya mayar da martani ta shafinshi na Twitter.



Sanata Dino Melaye ya rubuta cewa, "Game da hukuncin kotun sauraren kararrakin Zabe. Ko da ace nine na yi nasara, (abokan takarata) Zasu je kotun daukaka kara. Ba za'a iya kwace mana hakkin mu ba. Zamu je kotun daukaka kara. Za'a yi sabon zabe a Kogi a mazabar kogi ta yamma saboda zan zama gwamna. Maganar kujerar sanata ta ban kaduba.

Mahakurci mawadaci...Na kusa zama gwamnan Kogi.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment