Monday, 5 August 2019

Kakakin majalisar Dattijai ya tafi aikin Hajji

Kakakin majalisar Dattijai, Ahmad Lawal ya tafi kasar Saudiyya a yau, Litinin inda zai yi aik8n Hajjin bana tare da sauran musulmin Duniya.Me bashi shawara akan harkar watsa labarai, Mr Ola Awoniyi ya fitar da sanarwar ga manema labarai kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Ya kara da cewa, Lawal zai yiwa Najeriya addu'ar zaman lafiya, hadin kai da ci gaba yayin aikin hajjin sannan zai kuma wa majalisar tarayya addu'ar samun nasara da ci gaba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment