Thursday, 29 August 2019

Kalli abinda Ronaldo yayi da abinda yace bayan da Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gaba na UEFA da ya dauki hankula

Bayan da abokin takararshi, Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gaba na UEFA, An ga Cristiano Ronaldo ya canja fuska a Monaco.
Bayan dawowar Messi daga amso kyautar, ya dawo ya gaisa da Van Dijk saidai wasu sun lura da cewa Ronaldo ya canja fuska.


Saidai duk da haka a wannan haduwar da Ronaldo da Messi su kayi sun tattauna sosai inda aka ga suna hada kawuna suna magana, alamar da wasu ke cewa tana nuna yanda suka yi kewar juna.

Tun bayan da Ronaldo ya bar Real Madrid, basu taba haduwa shi da Messin a bainar jama'a ba kamar haka.

Da yake magana da 'yan jarida Ronaldo ya bayyana cewa, Tabbas suna da kyakkyawar dangantaka shi da Messi.

Yace bamu taba cin abinci tare ba amma ina fatan nan gana zamu kai ga yin hakan.

Abune me dadi kasancewa cikin tarihin kwallon kafa, ina nan shima kuma yazo,inji Ronado.

Ya kara da cewa Ni da Messi mun shafe shekaru 15 muna gasa da juna, hakan bai taba faruwa ba a tarihin kwallon kafa, ba abune me sauki ba, kuma na yi kewar yin kwallo a Sifaniya.

A Monacon dai An ga wasu Hotunan Ronaldo da Messi inda suka kayatar da masoyansu sukaita watsa su a shafukan sada zumunta.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment