Friday, 9 August 2019

Kalli yanda Bayern Munich ta ci wata kungiya 23-0 amma 'yan kungiyar basu damu ba

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta yiwa kungiyar kwallin kafa ta FC Rottach-Egern cin rabani da yaro na 23-0 a wasan sada zumunta da suka buga jiya, Alhamis.Yawan kwallayen ya bayar da mamaki sosai dan kuwa koda sanduna aka ajiye a filin watakila iya cin da Muncih zata musu kenan.

Lewandowski, Muller, Goretzka, Wriedt duk sunci kwallaye 3 kowannensu a wasan sannan sai Tolisso da yaci kwallaye 4 shi kadai, Singh, Sanchez, Dajaku, Gnabry, Bollenberger, da Dietrich kuwa sun ci kwallaye 1 kowannen su, 'yan wasan Munich 10 ne suka ci kwallaye a wasan.

Kungiyar dai karamar kungiyace amma wannan bai sa Munich ta tausaya mata ba, Munich ta hadu da manyan kungiyoyi irinsu Madrid kuma ta cisu a wasannin sada zumunta saidai itama ta hadu da daidai da ita a wasan da suka buga da Dortmund na cin kofin Super Cup na Jamus inda aka ci su 2-0.

Wani abin mamaki shine bayan tashi daga wasan, 'yan kungiyar Rottach-Egern din basu damu da cin da aka musu ba dan kuwa sun rika rububin daukar hoto da 'yan wasan na Munich.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment