Saturday, 3 August 2019

Kalli yanda Mbappe ya hana Neymar daukar hoto da sauran 'yan wasan PSG

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta lashe kofin Super Cup na Faransa bayan fata lallasa Rennes da ci 2-1 a wasan da suka buga yau. Mbappe da Dimaria ne suka ci mata kwallayen nata 2.
Tauraron dan kwallon PSG, Neymar ya je filin wasan amma be samu buga wasan ba saboda jiyyar gwiwarshi da yake.

Bayan kammala wasan, Neymar ya shigo fili inda ya karbi kyautar da ake baiwa 'yan wasa, saidai yaki shiga hoton 'yan wasan kungiyar da zasu dauka.

Marcos Verratti ne ya jawo Neymar cikin hoton saidai daga baya Mbappe ya ture Neymar gefe inda aka dauki hoton babushi, wannan abu ya dauki hankulan mutane sosai.

Saidai bayan kammala wasan, Neymar ya saka hotonshi tare da Mbappe a shafinshi na sada zumunta.

Kamin a fara wasan dai Mbappe ya bayyana cewa ya gayawa Neymar cewa yana sonshi kuma baya so ya bar kungiyar.

Sannan shima ya karyata rade-radin da ake na cewa zai bar PSG inda yace yana nan babu inda zashi.Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment