Friday, 30 August 2019

Kar fa ku sake tunzurani>>Ronaldo ya gargadi 'yan Atletico Madrid

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya gargadi magoya bayan Atletico Madrid da kada a wannan karin ma su sake yin abinda suka mai a baya yayin wasan gasar Champions League.A bara ne dai magoya bayan Atletico Madrid suka rika wa Cristiano Ronaldo ehon me yiwa mata fyade da kuma na kiyayya bayan da Atletico Madrid din ta lallasa Juventus da ci 2-0 a zagayen farko na wasan da suka buga, Ronaldo dai a wancan lokacin ya mayar musu da martani ta hanyar daga yatsu biyar watau alamar sau biyar ya dauki kofin na Champions League. Sannan kuma a zagaye na biyu ba wasan,Ronaldo ya hukunta Atletico Madrid da cin kwallaye 3 ringis shi kadai.

To gashi kuma a bana ma an sake hada kungiyoyin biyu a rukuni daya.

Wannan dalili yasa Ronaldo ya aikewa da magoya bayan Atletico Marid da sakon cewa kada a wannan karin ma su rika mai kalaman kiyayya.

Yace wasane me zafi zai kasance tsakaninsu. Kuma Atletico Madrid kungiyace me kyau, yasansu sosai dan kuwa ya zauna a real Madrid na tsawon lokaci.

Da yake magana akan kungiyar daya kamata ace ta lashe kofin na Champions League, Ronaldo yace babu kungiyar da a wannan karin bata yi shiri me kyau na ganin ta dauki kofinba.


Amma yana sa ran a wannan karin ya zama nasu duk dadai yasan cewa shine kofin da ya fi kowane wahalar ci kuma yawanci, kungiyar da aka fi so ba itace ke daukarshi ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment