Pages

Friday 16 August 2019

Kiris ya rage tsuntsaye su kifar da jirgi dauke da mutane 230

Wani jirgin sama samfurin Airbus dauke da mutane 230, ya yi saukar gaggawa a wata gonar masara a birnin Moscow na Rasha, bayan ya ci karo da garken tsuntsaye a sararin samaniya, yayinda gwamnatin kasar ta bayyana matukin jirgin a matsayin gwarzo.





Jirgin na Airbus mai lamba A321 ya gamu da hatsarin ne jim kadan da tashinsa daga filin jiragen sama na Zhukovsky na birnin Moscow da zummar isa yankin Crimea a safiyar wannan Alhamis.

Bayanai na cewa, injin jirgin ya zuko tarin tsuntsayen cikinsa, lamarin da ya tilasta wa tawagar matukan jirgin yanke shawarar saukar gaggawa a gonar masara da ke da nisan kilomita guda daga wurin da ya tashi, yayinda injin ya kashe kansa, sannan kuma giyarsa ta cije.

Tuni aka kwashe fasinjoji 226 da tawagar matuka 7 daga wannan jirgi, inda aka yi amfani da tsanin balan-balan wajen kwashe su.

Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Rasha ta ce, an garzaya da fasinjoji 23 zuwa asibiti amma babu wanda ya samu mummunan rauni daga cikinsu, face wata tsohuwa mai shekaru 69 da rauninta ya dare na kowa.


Fasinjojin dai sun jinjina wa matukin jirgin mai shekaru 41, inda suka bayyana shi a matsayin gwarzo, lura da bajintarsa ta ceton rayukansu a wannan Alhamis.

Ita ma fadar gwamnatin Kremlin ta yaba wa wanann matukin jirgin.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment