Sunday, 4 August 2019

Kuma dai: Wani dan ta'adda ya sake kai hari a Amurka inda ya kashe mutane 9

Kasa da awanni 24 bayan harin da wani dan ta'adda ya kai El Paso na kasar Amurka inda ya kashe mutane a kalla 20 sannan 22 suka samu raunuka, an sake samun wani dan ta'addan da ya kai hari Dayton na jihar Ohio.
Dan bindigar ya kashe mutane 9 da jikkata wasu 16 sannan 'yansanda sun bayyana cewa shima sun kasheshi.

Lamarin ya farune a kusa da wata mashaya inda yaje ya budewa mutane wuta.

BBC ta ruwaito cewa mutane sun rika gudun tsira yayin harbin sannan 'yansanda da jami'an FBI sun mamaye kan tituna da motocin agaji.

A yanzu dai mutane akalla 30 kenan suka mutu daga jiya zuwa yau a hare-haren 'yan bindigar wanda 'yan ta'addan kasar Amurkar suka kai.

'Yansandan dai sun bayyana cewa zuwa yanzu basu gano cikakken bayanai akan dan ta'addar ba.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zasku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment