Wednesday, 14 August 2019

Kungiyar Shi'a ta kasar Indiya tace zata biya kudin kulawar da za'awa Zakzaky a kasar


'Yan shi'ar kasar India zasu biya kudin jiyyar Zakzaky
Rahotanni dake fitowa daga kasar India na cewa wata kungiyar 'yan Shi'a ta kasar me suna, Anjuman e-Haideri ta ce zata dauki nauyin kudin aikin da za'awa shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi, IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarshi, Zeenat a kasar.A ranar Litininne aka fita da Zakzaky da matarshi daga Najeriya zuwa kasar India inda za'a musu aiki akan wasu cututtuka dake damunsu a asibitin Medanta dake birnin New Delhi.

Kungiyar ta Anjuman e-Haideri ta hannun Sakatarenta, Bahadur Naqvi  ta aikewa da shugaban kula da yin tiyata na asibitin Medanta, Dr. Naresh Trehan wasika inda tace zata biya duk kudin magani da aikin da za'awa Zakzaky.

Wasikar da aka aika ranar 12 ga watan nan na Augusta ta bayyana cewa, Za aiwa Shugabanmu Ibrahim El-Zakzaky wanda babban malamin addinine dake da dumbin mabiya a dukkan fadin Duniya aiki a asibitinku.

Kwamitin gudanarwa na kungiyarmu ya yanke shawarar biyan duk kudin aikin da za'awa Zakzaky a asibitinku, muna fatan zaku amince da hakan.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment