Sunday, 25 August 2019

Kusan rabin al'umar Najeriya ba sa samun wutar lantarki

Jami'in Cibiyar Kula da Tsaftataccen Fasahar Kere-Kere Mark Amaza a yayin wani taron tattaunawa da aka yi a jihar Kano dake arewacin kasar mai taen "Mafita Kan Makamashin Lantarki" ya fadi cewar 'yan Najeriya miliyan 93 wanda kusan rabin al'Umar kasar ne ba sa samun lantarki.


Amaza ya ce rashin samun isasshen lantarki ya sanya al'uma na cutar da dazuka kuma akwai bukatar a samarwa da jama'a isassshen makamashi wanda zai taimaka wajen saita tunaninsu.

Amaza ya ce "Da yawan al'umar Najeriya na amfani da itace waje girka abinci wanda hakan ke cutar da dan adam da kuma dazukan da ake da su." Ya kara da cewar idan ana so a samu mafita to dole ne a samar da makamashi mai sabuntuwa.

Kwararru sun ce sakamakon karuwan jama'ar najeriya kuma ba sa samun lantarki ya sanya an lalata sama da rabin dazukan dake kasar a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Ana yawan samun katsewar lantarki a kasar dake fama da matsaloli da yawa. Al'uma na amfani da injina don samun wuta a gidajensu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment