Friday, 9 August 2019

Kwallon da Messi ya ci Liverpool ta zama kwallon mafi kayatarwa ta UEFA ta shekara


Kwallon da Messi ya ci Liverpool daga bugun tazara
Kwallon da tauraron dan kwallon kungiyar Barcelona, Lionel Messi yaci Liverpool daga bugun tazara a wasan zagayen farko na kusa dana karshe da suka buga ce ta zama kwallon mafi kyawu ta hukumar UEFA.

A wasan da Barcelona ta ci Liverpool 3-0, Messi ya ci kwallaye 2.

Saidai a zagaye na biyu labari ya canja inda Liverpool ta lallasa Barca da ci 4-0.

Sunan Messi dai na cikin taurarin 'yan kwallon gaba na shekara na UEFA.

Saidai bayan bayyana wannan kwallo a matsayin kwallon shekara ta UEFA, magoya bayan liverpool sun rika wa Messin ba'a da cewa an bashine dai kawai dan ya dan ji dadi saboda rashin nasarar da yayi a wannan kakar.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment