Thursday, 15 August 2019

Liverpool ta ci Kofin Zakaran Zakaru na Turai bayan doke Chelsea


Golan Liverpool Adrian
Liverpool ta dauki kofin Zakaran Zakaru na Turai, wato Super Cup a karo na hudu a tarihinta, bayan da ta yi galaba a kan Chelsea da ci 5-4 a fanareti, bayan sun yi canjaras 2-2 a tsawon fafatawar wa'adi, a Istanbul.


Mai tsaron ragar Liverpool Adrian ne ya haramta wa Tammy Abraham na Liverpool daga ragarssa, wanda hakan ya ba wa Zakarun na Turai nasara.
Chelsea ce ta fara jefa kwallo a raga a minti 36 da shiga fili ta hannun Olivier Giroud, amma Sadio Mane ya farke Mané, miti uku bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Kasancewar kungiyoyin suna kunnen doki 1-1 har cikar lokacin ka'ida na minti 90, wannan ya sa aka tafi lokacin raba-gardama na minti 30.
A kashin farko na wannan lokacin na raba-gardama wato minti 15 na farko ne sai, Mane ya ci wa Liverpool bal ta biyu a daidai minti 95.
Chelsea ta samu bugun fanareti inda Jorginho ya bugu kuma ya ci a minti na 101, wanda hakan ya mayar da wasa 2-2, har aka kammala lokacin, abin da ya sa aka tafi bugun fanareti na fitar da gwani, inda Liverpool ta yi nasara.
Liverpool ta yi wannan nasara ne wata biyu bayan Jurgen Klopp ya jagorance ta ta dauki kofin Zakarun Turai, a lokacin da ta doke Tottenham 2-0 a wasan karshe.
A tarihin gasar kofunan Turai, wasa tsakanin kungiyoyin biyu yakan kasance da zafi, wanda a karawa 10 da suka yi a baya, guda daya ce kawai aka yi nasara da yawan kwallon da ya wuce daya.
Haka kuma abin ya kasance a ranar Larabar nan da dare, inda kungiyoyin biyu suka yi ta gumurzu tsawon minti 20, a wasan da ya kai kusan karfe 1 na dare a agogon Istanbul, kafin a samu gwani.
A karshe dai Adrian ya barar wa da Chelsea fanaretin da golan Liverpool Adrian ya hana ci, Reds din suka ci kofinsu na farko na wannan sabuwar kaka.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment