Saturday, 24 August 2019

Liverpool ta lallasa Arsenal da ci 3-1: Nicolas Pepe ya wuce Van Dijk da kwallo bayan wasanni 50 ba'a samu wanda yayi hakan ba

A wasan da suka buga yau na gasar Premier League, Liverpool ta lallasa Arsenal da ci 3-0 inda Salah ya ci kwallaye 2 sai kuma Matip da yaci kwallo ta 3.
Dayar Kwallon da Salah ya ci da Penalty Wadda David Luis ya jawo wa Arsenal wannan jangwangwama bayan da ya jawo rigar Salah ta dauki hankula inda saida aka duba VAR kamin yanke hukunci.

Bayan wasan Luis ya koka akan bugun Penaltin inda yace ko Salah din da suka yi magana ya gayamai cewa shi be jima ya tabashi ba.

Dan kwallon Arsenal Nicolas Pepe ya haskaka sosai a wasan duk da cewa basu yi nasara ba inda ya gogewa Virgil Van Dijk Hadda, ya zama dan kwallo na farko da ya fara wuceshi da kwallo a gasar Premier League bayan da Van Dijk din ya buga wasannin gasar 50 ba tare da samun wanda ya wuceshi da kwallo ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment