Wednesday, 7 August 2019

Liverpool ta sayo Adrian

Kungiyar Liverpool ta sayo golan Ispaniya mai wasa a West Ham United Adrian San Miguel del Castillo.


Bayanan da aka fitar daga Kungiyar Liverpool sun tabbatar da cewa an yi yarjejeniya da Adrian inda ya maye gurbin Simon Mignolet.

Adrian ya fara wasa a kungiyar West Ham United a shekarar 2013 inda ya halarci wasanni 150 a cikin shekaru 6.

Ba a bada cikakken bayani game da tsawon shekarar yarjejeniyar da dan wasan mai shekaru 32 ya yi da kungiyar ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment