Thursday, 8 August 2019

Lukaku ya tafi birnin Milan don tattaunawa da Inter


Romelu Lukaku
Inter Milan na dab da daukar dan wasan Manchester United Romelu Lukaku bayan da suka kara farashin da suka taya shi.


A watan Yuli, United ta yi watsi da tayin fan miliyan 54 da Inter ta yi kan Lukaku, wanda kulob din ya ci tararsa bayan da ya yi fashin atisaye ba tare da izini ba ranar Talata.
Dan wasan na Belgium, mai shekara 26, ya shafe kwana biyu yana atisaye a tsohon kulob dinsa a Anderlecht.
Wakilin Lukaku, Federico Pastorello, ya je London ranar Laraba a wani yunkurin na shawo kan batun makomar dan kwallon.
Daga bisani kuma Pastorello ya wallafa wani bidiyo a shafin Instagram tare da Lukaku a wani jirgin sama da taken: "Muna shirin tashi. Kuma birnin Milan muka nufa."
Inter da kuma Juventus sun yi rige-rigen daukar dan wasan, wanda bai buga wasa ko daya ba a wasannin shirin kakar bana da United ta yi saboda raunin da ya yi fama da shi.
A baya dai Antonio Conte ya tabbatar da cewa dan wasan na sahun gaba a jerin 'yan kwallon da yake so, yana mai cewa: "Ina daukarsa a matsayin dan wasan da zai inganta tawagarmu".
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment