Wednesday, 7 August 2019

Ma'aikacin kwastam yaki karbar cin hancin miliyan 1 da barayin miyagun kwayoyi suka bashi


Hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Customs ta kama wasu mutane 5 a jihar Rivers da laifin fasa kwantaina da satar kwayoyin Tramol da sauransu.

Kontrolan dake kula da yankin, Galadima Sa'idu ne ya bayyanawa manema labarai haka inda yace wadanda suka kama din sun kware wajan fasa kwantainonin kayan da aka kwace ake ajiyarsu a rumbun Custom din.

Yace sun zo da motoci inda suka zuba magungunan da suka sata a ciki amma an kamasu an kuma kwace magungunan.

Ya kara da cewa masu laifin sun yi yunkurin baiwa wani ma'aikacin kwastam din cin hancin miliyan daya dan ya barsu su wuce, an bashi umarnin ya amsa dan a kara samun hujja akansu inda daga baya aka kamasu.

Yace abin takaicine a yayin da hukumar kwastam ke kokarin kawar da matsalolin shigo da gurbatattun kaya amma wasu na nan burinsu shine su karya irin wannan doka.

Yace hukumar ta kwastam ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan tabbatar da aikinta ta yanda ya kamata ba.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment