Sunday, 4 August 2019

Man City ta doke Liverpool inda ta dauki kofin Community Shield: Zaka so ganin Kwallon da Kyle Walker ya cire

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sake daukar kofi a hannun Liverpool a wasan da suka buga da yammacin yau inda ta lashe kofin Community Shield bayan cin Liverpool 5-4 a bugun daga kai sai gola.Raheem Sterling ne ya ciwa Man City wasa sannan daga baya ana gab da tashi Joel Matip ya ciwa Liverpool kwallo wanda a haka aka tashi wasan kunnen doki 1-1.

Hakan tasa aka je bugun daga kai sai gola wanda a nanne Man City ta fitar da Liverpool.

Abubuwan da suka dauki hankula sosai a wasan sune.

Kwallon da Mohamed Salah ya so ci amma Kyle Walker ya fito da ita kamin ta shiga raga, kwallon ta wuce gola, raga kawai zata shiga Walker ya fito da ita waje.

Kalli kwallon a kasa:Sabon dan wasan Manchester City, Rodrigo Hern├índez Shima ya dauki hankula sosai dan kuwa ya taka rawar gani inda duk kusan kwallayen da ya bayar sun kai ga kafafun wanda ya baiwa sannan a wasanshi na farko a kungiyar ya daga kofi, wannan yasa shima akaita maganarshi.

Hakanan an rikawa golan Liverpool, Alisson ba'a inda wasu ke ganin be taka rawar a zo a gani ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zasku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment