Saturday, 10 August 2019

Man United ce tafi kashe kudi wajan sayen 'yan wasa a Ingila

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce ta shiga gaba wajan kashe kudi mafi yawa a gasar Premier League wajan sayen 'yan wasa a kasuwar da aka kulle ranar Alhamis din data gabata.Gaba daya kungiyoyin Premier League sun kashe Fan Biliyan 1.4 ne wajan sayen 'yan wasa a bana.

Shekaru hudu kenan kungiyoyin na Premier League na kashe sama da Biliyan 1 wajan sayen 'yan wasa.

Man United ta kashe fan Miliyan 148 wajan sayen 'yan wasa wanda hakan yasa ta zama ta daya wajan kashe kudi, Man United ta sayi Harry Maguire kan Fan miliyan 80 wanda shine dan wasa mafi tsada da aka siyo a Ingila.

Aston Villa da suka fito data Relegation ne suka zo na biyu wajan kashe kudi inda suka kashe fan miliyan 144.5 wajan sayen 'yan wasa 12.

A baya anyi rade-radin cewa Arsenal miliyan 45 kawai gareta amma wannan rade-radi yazo karshe bayan da suka sayo Nicolas Pepe daga Lille akan fan miliyan 72 wanda ya zama dan wasa mafi tsada data taba siye inda ya zarta Pierre-Emerick Aubameyang da suka sayo akan fan miliyan 55 a shekarar 2018.

Manchester City ta kashe fan miliyan 122.5 wajan saye Joao Cancelo da Rorigo.

Everton da Tottenham ne kungiyoyi bitu da suka kashe sama da fan miliyan 100 wajan sayen 'yan wasa a bana.

Kungiyar Norwich ce ta kashe kudi mafi karanta wajan sayen 'yan wasa a bana inda ta kashe fan miliyan 1.1.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment